Revelation of John 8

Hatimi na Bakwai da Kaskon Zinariya

1Saʼad da ya buɗe hatimi na bakwai, sai aka yi shiru a sama na kusan rabin saʼa. 2Sai na ga malaʼiku bakwai da suke tsayawa a gaban Allah, a gare su kuwa aka ba da ƙahoni bakwai.

3Wani malaʼika, da yake da kaskon zinariyar da ake zuba turare, ya zo ya tsaya kusa da bagaden. Aka ba shi turare da yawa don yǎ miƙa tare da adduʼoʼin dukan tsarkaka a bisa bagaden zinariya a gaban kursiyin. 4Hayaƙin turaren tare da adduʼoʼin tsarkaka, suka hau zuwa gaban Allah daga hannun malaʼikan. 5Sai malaʼikan ya ɗauki kaskon, ya cika shi da wuta daga bagaden, ya kuma wurga shi bisan duniya; sai aka yi ta yin tsawa, ƙararraki, walƙiya, da kuma girgizar ƙasa.

Ƙahoni

6Sai malaʼiku bakwai ɗin nan da suke da ƙahoni bakwai suka shirya don su busa su.

7Malaʼika na fari ya busa ƙahonsa, sai ga ƙanƙara da wuta haɗe da jini, aka kuma wurga su bisan duniya. Kashi ɗaya bisa uku na duniya ya ƙone, kashi ɗaya bisa uku na itatuwa suka ƙone, dukan ɗanyar ciyawa kuma ta ƙone.

8Malaʼika na biyu ya busa ƙahonsa, sai ga wani abu kamar babban dutse mai cin wuta, aka jefa cikin teku. Kashi ɗaya bisa uku na teku ya zama jini, 9kashi ɗaya bisa uku na halittu masu rai da suke cikin tekun suka mutu, kashi ɗaya bisa uku kuma na jiragen ruwa kuma suka hallaka.

10Malaʼika na uku ya busa ƙahonsa, sai wani babban tauraro mai cin wuta kamar toci, ya fāɗi daga sararin sama, a kan kashi ɗaya bisa uku na koguna da kuma a bisa maɓulɓulan ruwa—  11sunan tauraron kuwa Maɗaci. Kashi ɗaya bisa uku na ruwaye ya zama mai ɗaci, mutane da yawa kuma suka mutu saboda shan ruwan, don ɗacinsa.

12Malaʼika na huɗu ya busa ƙahonsa, sai aka bugi kashi ɗaya bisa uku na rana, kashi ɗaya bisa uku na wata, da kashi ɗaya bisa uku na taurari, har kashi ɗaya bisa uku nasu ya duhunta. Kashi ɗaya bisa uku na yini ya kasance babu haske, haka ma kashi ɗaya bisan uku na dare.

13Yayinda nake ƙallo, sai na ji gaggafar da take tashi sama a tsakiyar sararin sama ta yi kira da babbar murya ta ce: “Kaito! Kaito! Kaiton mazaunan duniya, in an yi busan sauran ƙahonin da malaʼikun nan uku suke shirin busawa!”

Copyright information for HauSRK